John 7

Yesu Ya Tafi Bikin Bukkoki

1Bayan wannan, sai Yesu ya yi ta zagawa a cikin Galili, da ganga bai yarda yǎ je Yahudiya ba domin Yahudawa a can suna nema su kashe shi. 2Amma saʼad da Bikin Bukkokin Yahudawa ya yi kusa, 3sai ʼyanʼuwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka bar nan ka tafi Yahudiya, don almajiranka su ga ayyukan banmamaki da kake yi. 4Ba wanda yake so a san shi da zai yi abu a ɓoye. Da yake kana yin waɗannan abubuwa, sai ka nuna kanka ga duniya.” 5Domin ko ʼyanʼuwansa ma ba su gaskata da shi ba.

6Saboda haka Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna; amma a gare ku kowane lokaci daidai ne. 7Duniya ba za ta iya ƙinku ba, amma ni take ƙi domin ina shaida cewa ayyukanta mugaye ne. 8Ku ku tafi Bikin, ba zan in haura zuwa wannan Bikin ba yanzu, domin lokacina bai yi ba tukuna.” 9Da ya faɗa haka, sai ya dakata a Galili.

10Amma fa, bayan ʼyanʼuwansa suka tafi Bikin, shi ma ya tafi, ba a fili ba, amma a ɓoye. 11A Bikin kuwa, Yahudawa suka yi ta nemansa, suna cewa, “Ina mutumin yake?”

12A cikin taron kuwa aka yi ta raɗe-raɗe game da shi. Waɗansu suka ce, “Shi mutumin kirki ne.”

Waɗansu kuwa suka ce, “Aʼa, ai, ruɗin mutane yake.”
13Amma ba wanda ya ce kome a fili game da shi don tsoron Yahudawa.

Yesu Ya Koyar a Bikin

14Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, saʼan nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa. 15Yahudawa suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya wannan mutum ya sami wannan sani haka ba tare da ya yi wani karatu ba?”

16Yesu ya amsa, ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni. 17Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana. 18Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi. 19Ashe, ba Musa ba ne ya ba ku Doka? Duk da haka ba ko ɗayanku da yake kiyaye Dokar. Me ya sa kuke nema ku kashe ni?”

20Taron suka amsa suka ce, “Kana da aljani, wane ne yake so yǎ kashe ka?”

21Yesu ya ce musu, “Na yi abin banmamaki ɗaya, dukanku kuwa kuka yi mamaki. 22Duk da haka, domin Musa ya bar muku kaciya (ko da yake a gaskiya, ba daga wurin Musa ne ya fito ba, sai dai daga wurin kakannin kakanninku), ga shi kuna yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci. 23To, in za a iya yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci don kada a karya dokar Musa, don me kuke fushi da ni saboda na warkar da mutum a ranar Asabbaci? 24Ku daina yin shariʼa bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shariʼa bisa ga adalci.”

Shin, Yesu shi ne Kiristi?

25A nan ne fa waɗansu mutane daga Urushalima suka fara tambaya suna cewa, “Ashe, ba wannan mutum ne suke nema su kashe ba? 26Ga shi nan yana magana a fili, su kuma ba su ce masa uffam ba. Ko hukumomi sun yarda cewa shi ne Kiristi? 27Mun dai san inda mutumin nan ya fito; amma saʼad da Kiristi ya zo ba wanda zai san inda ya fito.”

28Yesu yana cikin koyarwa a filin haikali ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “I, kun san ni, kun kuma san inda na fito. Ban zo don kaina ba, sai dai shi da ya aiko ni mai gaskiya ne. Ba ku san shi ba, 29amma na san shi, domin ni daga wurinsa ne, kuma shi ya aiko ni.”

30Da jin haka, sai suka yi ƙoƙari su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna. 31Duk da haka, da yawa a cikin taron suka ba da gaskiya gare shi. Suka ce, “Saʼad da Kiristi ya zo, zai yi abubuwan banmamaki fiye da na wannan mutum ne?”

32Farisiyawa suka ji taron suna raɗe-raɗen waɗannan abubuwa game da shi. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki masu gadin haikalin su kama shi.

33Sai Yesu ya ce, “Ina tare da ku na ɗan ƙanƙanin lokaci ne kawai, saʼan nan zan koma wurin wanda ya aiko ni. 34Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba; inda nake kuwa, ba za ku iya zuwa ba.”

35Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina mutumin nan yake niyyar tafiya da ba za mu iya samunsa ba? Zai je wurin mutanenmu da suke zaune warwatse a cikin Helenawa, yǎ kuma koya wa Helenawa ne?” 36Me yake nufi da ya ce, “Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba,” da kuma “Inda nake, ba za ku iya zuwa ba?”

37A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yǎ zo wurina yǎ sha. 38Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa.” 39Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yǎ zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.

40Da jin kalmominsa, waɗansu mutane suka ce, “Ba shakka, mutumin nan shi ne Annabin.”

41Waɗansu suka ce, “Shi ne Kiristi.”

Waɗansu har wa yau suka ce, “Yaya Kiristi zai fito daga Galili?
42Nassi bai ce Kiristi zai fito daga zuriyar Dawuda, daga kuma Betlehem garin da Dawuda ya zauna ba?” 43Sai mutanen suka rabu saboda Yesu. 44Waɗansu suka so su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi.

Rashin Bangaskiyar Shugabannin Yahudawa

45A ƙarshe masu gadin haikali suka koma wurin manyan firistocin da Farisiyawa, waɗanda suka tambaye su cewa, “Don me ba ku kawo shi nan ba?”

46Sai masu gadin suka ce, “Kai, babu wanda ya taɓa magana kamar wannan mutum.”

47Sai Farisiyawa suka amsa cikin fushi suka ce, “Af, kuna nufi har da ku ma ya ruɗe ku ke nan? 48Akwai wani daga cikin masu mulki ko cikin Farisiyawan da ya gaskata da shi? 49Aʼa! Sai dai wannan taron da ba su san kome game da Doka ba-laʼanannu ne.”

50Nikodimus, wanda ya je wurin Yesu dā, wanda kuma yake ɗayansu ya ce, 51“Ashe, dokarmu takan hukunta mutum ba tare da an fara ji daga bakinsa game da abin da yake yi ba?”

52Sai suka amsa suka ce, “Kai ma daga Galili ne? Bincika ka gani, za ka iske cewa ba annabin da zai fito daga Galili.”

[Rubuce rubucen farko farko da kuma mafi ingancin da aka fi dogara da su tare da waɗansu shaidu na dā ba su da Yohanna 7.53–8.11.]

53Sai kowannensu ya koma gidansa.

Copyright information for HauSRK